Kotu ta tabbatar da zaben Ikpeazu

Wata babbar kotun tarayya dake garin Owerri ta jihar Imo ta tabbatar da zaben da akayi ma gwamnan Abia Okezie Ikpeazu. Mai shari’a A. I Allagoa shine ya yanke hukuncin yau juma’a 8 ga watan nan bayan da lauyoyin masu kara suka kasa gamsar da kotun kewar takardun biyar haranjin gwamnan na boge ne. Jaridar Vanguard ce ta ruwaito hakan. Daga baya ne sai kotun ta tabbatar da cewa takardun na shedar biyan harajin ba na boge bane sannan kuma ta kori karar. Shi dai mai shari’a Okon Abang da a ranar 27 ga watan da ya gabata ne ya bayyana cewa gwamnan na Abia Ikpeazu ba halattacen gwamnan jihar bane sakamakon gano shi da akayin da mikawa jam’iyyar sa ta PDP shaidar biyan haraji da boge gabanin zabukan fidda gwani a jihar cikin shekarar 2014. Haka zalika mai shari’ar ya umurci Ikpeazu da ya sauka daga mulki sannan kuma ya umurci hukumar zabe mai zaman kanta da ta ba Uche Oga takardar shedar cin zabe a matsayin sa na wanda yazo na biyu a wancen zaben fitar da gwanin.PDP Abuja

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s